ABNA: Kotun dake sauraran shari'ar tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir taki amincewa da bukatar lauyoyinsa na bayar da belinsa.
Jaridar Al-arabie Jaded ta bayar da rahoton cewa, kotun da sauraran shari'ar hambararren shugaban kasar Sudan ta ki amincewa da bukatar lauyoyin Al-bashir na bayar da belinsa ta hanyar ajiye wasu kadarori,
Kotun dai na tuhumar Al-bashir da tara dukiya ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma ajiye ta a cikin gida.
Tsohon shugaban kasar ta Sudan ya amince da karfar rashawa daga yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bn Salman.
Masu bincike a kasar ta Sudan na zargin shugaba Al-Bashir da karbar kudi da suka kai dalar Amurka miliyan 90 daga yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman
Omar el-Bashir wanda ke tsare a wani gidan yari da ke birnin Khartum, hukumar mulkin sojan kasar na zarginsa ne da tara makudan kudade fiye da dalar Amurka miliyan dari da 13 a yayin wani samame da suka kaddamar a gidansa, jim kadan bayan hambarar da shi daga kan mulki.
.............
300